MDD ta damu matuka akan hallaka fararen hula a Siriya

MDD ta damu matuka akan hallaka fararen hula a Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ta damu matuka game da karuwar tashin hankali a arewa maso yammacin Siriya.

Da yake magana a taron manema labarai na yau da kullum a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya, Mataimakin Sakatare Janar Farhan Haq ya ce, "Rikicin da ke faruwa ya yi sanadiyyar mutuwar da jikkata fararen hula da dama, ciki har da mata da yara da yawa, a cikin makonnin da suka gabata." 

Haq ya bayyana cewa a matsayinsu na Majalisar Dinkin Duniya sun damu matuka game da karuwar tashe-tashen hankula a yankin, don haka ya yi kira ga bangarorin da su dauki dukkan matakan kauce wa cutar da fararen hula kamar yadda dokar jin kai ta duniya ta tanada.

A Siriya, gwamnatin Bassar Assad da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu samun goyon bayan Iran sun kai hari a kauyen Iblin da ke kan iyakar yankin Idlib inda aka ayyanar da tsagaita wuta a ranar Alhamis, inda suka kashe fararen hula 7, ciki har da mace, da yara 3, da kuma fararen hula 3.

Majiyoyin ‘yan adawar sun kuma sanar da cewa jiragen yakin Rasha sun kai hare-hare a kauyukan Bara, İhsim da Mirayan da ke kudancin Idlib.


News Source:   ()