Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana rahoton ne yayin taron da ƙasashe da dama suka fara cikin makon jiya a birnin Riyadh na Saudiya, wanda kuma za a ƙarƙare a ranar Juma’a.
Ƙasashen na tattaunawa ne kan yadda za su daƙile gusowar Hamadar da ke ƙara girma saboda matsalolin da ayyukan ɗan Adam ke haifarwa da suka haɗa da ɗumamar yanayi, sare dazuka, da kuma ƙarancin saukar ruwan sama da ƙafewar na ƙarƙashin ƙasa a wasu yankuna.
Binciken ƙwararru ya gano cewar fiye da kaso 75 cikin 100 na faɗin kan tudu a sassan duniya sun fuskanci bushewar ƙasa da tsananin zafi daga shekarar 1970 zuwa 2020, fiye da yanayin da aka gani shekaru 30 gabanin lokacin da aka zayyana.
Wannan ce ta sanya masanan gargadin cewar, idan aka cigaba da tafiya a haka, to fa nan da ƙarshen ƙarnin da muke, kimanin mutane biliyan 5 ne za su fuskanci matsalolin gusowar Hamada, kuma iftila’in na fari zai fi ƙamari ne a sassan duniya da suka haɗa da akasarin nahiyar Turai, da yammacin Amurka, da Brazil da gabashin Asiya da kuma tsakiyar Nahiyar Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI