MDD ta bude asusun tara dala miliyan 100 don sake gina Falasdin

MDD ta bude asusun tara dala miliyan 100 don sake gina Falasdin

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga mambobin kungiyar da su tara dala miliyan 100 domin tallafawa sake gina yankunan Falasdinawa da rikici ya lalata.

Kodinetan bayar da agajin gaggawa na MDD a yankin Falasdinawa Lynn Hastings ta bayyana cewa an bude asusun tara tallafin gaggawa domin tara kudaden da za’a taimaka wajen sake gina Gaza, Kogin Jordan da Gabashin Kudus.

Tare da Babban Sakataren Janar na MDD António Guterres da karamin sakatare mai kula da bayar da agajin gaggawa Mark Lowcock, Hastings ta yi kira ga mambobin kungiyar da su tara dala miliyan 95 domin sake gina yankunan Falasdin da suka lalace sanadiyar hare-haren da Isra’ila ta kai yankunan.


News Source:   ()