MDD ta buƙaci Isra'ila ta kawo ƙarshen mamayar yankin Falasɗinu

MDD ta buƙaci Isra'ila ta kawo ƙarshen mamayar yankin Falasɗinu

Ƙudirin, wanda biyayya da shi ba dole ba ne, kuma Isra’ila ta bayyana shi a matsayin mai cike da ƙura-ƙurai da son zuciya, ya ta’allaka ne kan shawarar da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICJ, wadda ta ce mamayar da aka yi tun daga shekarar 1967 ta saɓa wa doka.

Ƙasashen 124 suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da wannan ƙudiri, 14 su ka nuna rashin amincewa a yayin da 43 su ka kauce wa kaɗa ƙuri’a.

Ƙasashen Larabawa ne su ka yi kira a gudanar da wannan taro na musamman, ƴan kwanaki bayan da gwamman jagororin duniya su ka hallara  a shelkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya domin tsara yadda za a gudanar da taron babban zauren Majalisar na wannan shekarar.

Bugu da ƙari,, matakin na zuwa ne makwanni gabanin cika shekara guda da harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya hadda yaƙin da ake yi a Gaza.

Ƙudirin, wanda shi ne mna farko da wakilan Falasɗinawa su ka gabatar a ƙarƙashin sabuwar damar da su ka samu a wannan shekarar, ta buƙaci Isra’ila ta kawo ƙarshen kasancewarta a yankin ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya kuma yi kira Isra’ila ta  yi biyayya da ƙudirin a cikin watanni 12. Waɗanda aka yi a baya sun bada watanni 6 ne kacal.

Isra’ila ta yi watsi da ƙudirin, tana mai cewa ya na cike da ƙura-ƙurai da son zuciya, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajenta, Oren Marmorstein ya wallafa a shafinsa X.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)