Kakakin ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya Thameen Al-Kheetan ya bayyana cewa, daruruwan mazauna Jenin ne suka tsere daga gidajensu yayin da sojoji suka ruguza wasu gidaje yayin wani gagarumin farmaki a Yamma da Kogin Jordan.
An kaddamar da aikin ne a cikin ‘yan kwanaki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki, wanda aka yi musayar Yahudawa da fursunonin Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila tun bayan wata 'yar gajeruwar sulhu a watan Nuwamban 2023.
Jami’an Isra’ila sun ce farmakin na Jenin an kaddamar da shi ne kan kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan Iran a sansanin ‘yan gudun hijira da ke makwabtaka da birnin, wanda ya kasance cibiyar kungiyoyin Falasdinawa masu dauke da makamai tsawon shekaru.
Sai dai ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wadanda aka kasha galibin mutanen da ba sa dauke da makamai ne, inda ya yi kira da a gaggauta kawo karshen tashin hankalin tare da dakatar da ci gaba da mamayar da Isra’ila ke yi.
Isra'ila ta mamaye Yammacin Kogin Jordan, wanda Falasdinawa ke so a matsayin kasa mai cin gashin kanta, tun bayan yakin Gabas ta Tsakiya da ya kunno kai a 1967, inda ta gina matsugunan yahudawa a wurin da galibin kasashen ke ganin hakan ya sabawa doka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI