Majalisar Dinkin Duniya MDD ta rataba hannu akan yarjejeniyar iyaka da Turkiyya ta yi da Libiya.
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya rataba hannu akan yarjejeniyar iyaka da Turkiyya ta yi da Libiya wanda aka sanya a kundin yarjeniyoyin MDD a matsayin sakin layi na 102 a ranar 30 ga watan Satumba.
A ranar 27 ga watan Nuwamba bara ne Turkiyya da Libiya baya ga hadakar soja da tsaro suka kuma ayyanar da yarjejeniyar iyakar teku wanda Majalisar Dinkin Duniya ta amince dashi.