MDD ta aike da kayayyakin abinci Siriya

MDD ta aike da kayayyakin abinci Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta aike da kayayyakin abinci har ton 625 domin rabawa mabuka da magidanta dake Idlib din kasar Siriya.

An tattabar da cewa tirelolin dake dauke da abincin da MDD ta bayar da umarnin aikawa dasu Siriya sun wuce kofar Cilvegozu dake yankin garin Reyhanli dake karkashin gundumar Hatay a kasar Turkiyya.

Daga cikin kayayyakin abinciccukan akwai garin fulawa, sukari, man dafa abinci, hatsi da kuma wasu nau'ukan abincin da ake karin kummalo dasu.

Tireloli dai guda 65 ne dauke da kayayyakin abinciccukan har ton dari 625 MDD ta bayar da umarnin kaiwa da rabawa mabukata a Idlib din Siriya.

An baiyana cewa kofar Cilvegozu ne kawai wanda kungiyoyin kasa da kasa ke iya bi domin aikawa da gudunmowa ga mabukatan kasar Siriya.

 


News Source:   ()