Jagororin ƙasashe sun yi jawabi ga taron, bayan da suka amince da wata yarjejeniya a game da makomar duniya, wadda aka cimma da zummar tabbatarwa tare da yauƙaƙa haɗin kai tsakanin ƙasashe, inda da dama ke kira da a gaggauta ba su damar amfana da kuɗaɗen da aka tanada don tinkarar sauyin yanayi.
Guterres ya shaida wa jagororin cewa, kalubalen sun ɗauki hanyar fin ƙarfin mahukunta, musamman ma yadda ci gaban fasahar zamani ke taimakawa wajen yaɗa bayanai marasa tushe a kan yanayi, lamarin da ke ta’azzara rashin yarda da rarrabuwar kawuna.
Firaministar Barbados, Mia Mottley ta jaddada kashedin Guterres a kan batun sake lale a game da yadda ake tafiyar da hukumomin duniya, ta inda za su iya tinkarar matsaloli tare da taimaka wa waɗanda su ka fi kasancewa cikin matukar buƙata.
Ƙungiyar yanayin, wanda ke tsara shirin makon yanayi ya zayyano taruka dabam-dabam har 900 masu nasaba da yanayi waɗanda za su gudana a wannan makon, waɗanda kamfanonin kasa-da-ƙasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatoci za su ɗauki nauyin shiryawa.
A waje ɗaya kuma a cikin wannan makon, shugaban Amurka, Joe Biden zai gabatar da jawabi a wani taro da ya samu halartar jaruma, kuma mai fafutukar kare muhalli, Jane Fonda da shugaban bankin duniya, Ajay Banga da sauransu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI