Kiran majalisar na zuwa ne, a dai-dai lokacin da matsaloli na yaƙe-yaƙe da sauran nau’ikan rikice-rikice, da kuma tasirin sauyin yanayi suka mamaye duniya, abinda ya sa ba za ta iya tunkarar matsalolin ba ita ƙadai.
Sabon shugaban hukumar kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher ya ce matsaloli sun yi wa duniya yawa, a don haka yana fargabar yadda za ta kaya a shekarar 2025 da ke tafe.
Yayin da yake ƙaddamar da rahoton nazarin ayyukan jin ƙai a duniya, Fletcher ya yi nuni da cewa Majalisar da abokan hulɗarta ba za su iya cimma kai agaji ga masu buƙata ba.
Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce aƙalla mutane miliyan 305 ne za su buƙaci agajin gaggawa a shekarar 2025.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI