MDD: Manyan kaburbura 8 da aka gano a Libiya abin tsoro ne

Majalisar Dinkin Duniya MDD ta bayyana ganin manyan kaburbura guda takwas a yankunan da dakarun halatacciyar gwamnatin Libiya ta karbe daga hannun mayakan Janar Khalifa Haftar a matsayin abin tsoro da tada hankali.

Kwamitin samar da lafiyar ta MDD  ta yada a shafinta ta twitter da cewa manyan kaburbura 8 da aka gano a yankunan da aka karbe daga hannun mayakan Haftar mafi yawa a garin Tarhuna abin tsoro ne.
Dokar kasa da kasa ta bayar da dama ga hukumomi da su yi bincike akan dukkanin kisan gillar da aka aikata domin daukar matakan da suka dace.

Jaridar Daily Sabah ta rawaito cewa  an gano manyan kuburbura a yankunan garin Tarhana da kuma kudu maso gabashin babban birnin kasar Tripoli bayan kwace yankunan daga hannun mayakan Janar Haftar ‘yan tawaye.

 

 

 


News Source:   www.trt.net.tr