MƊD ta zargi 'yan tawayen M23 da kashe kananan yara a gabashin Congo

MƊD ta zargi 'yan tawayen M23 da kashe kananan yara a gabashin Congo

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar, ya yi gargadin halin da ake ciki a gabashin ƙasar da ke ci gaba da yin ƙamari.

Mai magana da yawun ofishin kare hakkin bil adama Ravina Shamdasani, ta shaidawa manema labarai a birnin Geneva cewa, baya ga take hakkin dan adam da cin zarafi da M23 ke ci gaba da yi, su na kuma tilastawa kananan yara ɗaukar makamai.

Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta bukaci Rwanda da M23, da su tabbatar sun mutunta dokar kare hakkin dan adam da kuma dokokin jin ƙai na ƙasa-da-ƙasa.

Mayaƙan M23 da sojojin Rwanda sun ƙwace Goma da Bukavu, wato manyan biranen lardin Kivu ta Arewa da kuma Kudancin ƙasar.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, a kudancin Kivu, sama da mutane 150,000 ne aka tilastawa yin hijira.

Majalisar ta ce, Rwanda ta na da iko da kungiyar M23 kuma tana da sojoji aƙalla 4,000 da ke yaƙi tare da ‘yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)