Masu addu'oin dauke da firanni da kararrawa da kuma ayaba sun ziyarci wuraren ibadar Hindu domin gudanar da addu'oin samun nasarar ta a zaben da kasashen duniya suka mayar da hankali a kai tsakaninta da tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Wurin ibadar Thulasendrapuram dake jihar Tamil Nadu ya gamu da tarin mabiya addinin Hindu wadanda mazauna kauyen ne da kuma baki 'yan yawon bude ido.
Hotan Kamala Harris a kauyen kakaninta dake India © REUTERS/Francis MascarenhasAn haifi kakan Harris ta wajen uwa P.V. Gopalan ne a kauyen shekaru sama da 100 da suka gabata a Thulasendrapuram, kafin daga bisani ya yi kaura zuwa babban birnin Chennai a matsayinsa na babban jami'in gwamnati bayan ya yi ritaya.
Bayan gudanar da addu'oi daban daban, limamin wurin ibadar ya bayyana Harris a matsayin wadda za ta yi nasara, ya yin da ya rarraba hoda da toka ga wadanda suka halarci bikin addu'ar.
Rahotanni sun ce an rubuta sunan Harris a kan wani dutse dake wurin ibadar tare da sunayen wadanda suka bada sadaka da kuma sunan kakanta.
A kofar shiga wurin addu'ar, wani dan siyasar yankin Arulmozhi Sudhakar, ya kafa wani allon dake fatar nasarar 'yarsu a zaben na yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI