Turkiyya ta bayyana matukar damuwa game da hukuncin da Sabiya ta yanke na mayar da ofishin jakadancinta na Isra'ila zuwa birnin Kudus.
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta fitar da wata sanarwa a rubuce inda take cewa,
"Muna masu matukar damuwa akan hukuncin da kasar Sabiya ta yanke na mayar da ofishin jakadancinta a kasar Isra'ila zuwa Kudus"
Sanarwar da ta kara tunatar da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da yadda Isra'ila ke ci gaba da mamayar Kudus, inda ta kara da cewa,
"MDD ta ci gaba da jaddada cewa matukar ba'a mayar da tsarin Falasdin da iyakokinsu kamar yadda suke a shekarar 1967 ba, duk wani yunkuri da suka hada da mayar da ofishin jakadancin wasu kasashe na Isra'ila daga Tel Aviv zuwa Kudus lamurka ne da suka sabawa dokar kasa da kasa kuma goyon bayan ci gaba da ha'intar Falasdinawa ne."
Muna kira ga dukkan kasashe da su kaucewa irin wannan matakin tare da mutunta hanyoyin diflomasiyya ta MDD da zasu samar da lumana a yankunan baki daya.
Shugaban kasar Amurka a 'yan kwanakin da suka gabata ya bayyana cewa Kosova ta sulhunta da Isra'ila kuma Sabiya zata mayar da ofishin jakadancinta na Isra'ila zuwa Kudus.