An sanar da cewa a harin da mayakan kungiyar Taliban suka kai a barikin sojojin dake jihar Belh a Arewacin kasar Afghanistan sojoji biyar sun rasa rayukansu.
Mai magana da yawun barikin sojojin na 209 Muhammad Hanif Rizai ne ya bayyana cewa mayakan sun kai hari a barikin sojoji dake garin Chimtal a karkashin gundumar Belh dake arewacin kasar Afghanistan.
Ya kara da cewa a harin sojoji 5 sun rasa rayukansu inda wasu 2 kuma suka raunana.
Rizai ta kuma tabbatar da cewa an magance 7 daga cikin mayakan.
Sai dai shaidun gani da ido sun bayyana cewa sojoji 10 aka kashe kuma mayakan sun kame wasu 5 tare da yin awon gaba dasu.
Ita kuwa Taliban ta bayyana cewa sojoji 11 ne ta kashe a harin da ta kai.