Mayakan Hamas sun taru a gaban gidan Yahya Sinwar da ke Khan Younis

Mayakan Hamas sun taru a gaban gidan Yahya Sinwar da ke Khan Younis

Kamar yadda bayanai suka tabbatar, anan ne ake sa ran sakin wasu daga cikin Yahudawan da ke tsare a hannun hamas, bayan mika Agam Berger ga kungiyar agaji ta Red Cross a Jabalia.

Yadda dakarun Hamas suka tsaya gaban gidan Yahya Sinwar a Khan Younis Yadda dakarun Hamas suka tsaya gaban gidan Yahya Sinwar a Khan Younis © reuters

A ranar 17 ga watan Oktoban bara ne, harin saman da Isra'ila ta kaddamar a arewacin Gaza ya rutsa da Yahya Sinwar.

Tun da farko dai sai da Isra'ila ta gudanar da bincike domin tantance kwayoyin halittan shugaban na Hamas kafin tabbatar da mutuwarsa.

Kamar yadda bayanai suka a wancan lokacin, sakamakon farko-farko na gwajin kwayoyin halittar ya nuna cewa, Sinwar ɗin ne Isra'ila ta kashe kamar yadda ta tabbatar wa Amurka.

Isra'ila ta ɗauki gawar Sinwar zuwa Birnin Kudus domin gudanar da bincike a kanta bayan harin da ta kai cikin wani gida da shugaban na Hamas da muƙarrabansa ke ciki.

Dandazon mutanen da suka isa gidan Yahya Sinwar kenan a Khan Younis. Dandazon mutanen da suka isa gidan Yahya Sinwar kenan a Khan Younis. © reuters Baya ga dakarun Hamas da ke tsaye a kofar gidan Sinwar, akwa dubban mutane da ke kewaye da su, wadanda rahotanni suka ce suna jiran isowar Falasdinawan da Isra'ila ta sako daga gidajen yarinta.

Karo na uku kenan da aka yi musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu, tun daga lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)