Mayakan Haftar sun kaiwa wani jirgin ruwa hari a Libiya

Mayakan Haftar sun kaiwa wani jirgin ruwa hari a Libiya

An sanar da cewa mayakan Haftar da wasu sojin haya masu goya musu baya sun kaiwa wani jirgin ruwa hari a tashar jirgin ruwan Ras Lanuf dake kasar.

Kamar yadda ma'aikatar man kasar Libiya ta sanar a rubuce, mayakan haftar da wasu sojojin haya daga kasashen waje sun budewa wani jirgin ruwa da ya tunkari tashar jirgin ruwan, wuta da rokoki da gurnati.

An sanar da cewa suna hakon jirgin ruwa mai suna Muhammed Bey a tsibirin Komoro, lamarin da ya haifar da tsaikon sanyawa jirgin kaya.

Yankin gabashin kasar mai yawan albarkatun man kasar har kaso 80 cikin dari dake hannun kulawar mayakan Haftar sun kasasnce a rufe inda suka rinka kai hare-hare domin kalubalantar halastacciyar gwanmatin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a kasar.

Hukumar dake da alhakin hakar ma'adanan man kasar ta bayyana cewa sanadiyar hare-haren an samu raguwar gangar man da ake haka a rana lamarin dake haifar da hasarar dala miliyan 221.

 


News Source:   ()