Mayaƙan Huthi sun amince a ceto jirgin da suka yi luguden wuta

Mayaƙan Huthi sun amince a ceto jirgin da suka yi luguden wuta

Wannan na zuwa ne bayan ƴan tawayen na Huthi da ke samun goyon bayan Iran sun ƙaddamar da hari kan jirgin dakon man mallakin Girka a gaɓar ruwan Hodeida a makon jiya, inda nan take jirgin ya  kama da wuta, yayin da aka tsirar da jami’an da ke cikinsa.

Gwamnatin Iran ce ta shiga tsakani wajen cimma yarjejeniyar wucen-gadin bayan ƙasashen duniya da dama sun tsoma baƙi don ganin an tura wasu ƙananan jiragen ruwan da za su ceto jirgin dakon man da Huthi ta far masa.

Ƴan tawayen na Huthi sun ƙaddamar da yaƙi kan jiragen ruwan ƙasa da ƙasa da ke ratsawa ta tekun Maliya da kuma mashigin ruwan Aden, suna masu bayyana harin da suke kaiwa a matsayin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a daidai lokacin da ake gwabza yaƙi tsakanin Isra’ila da Hamas a Zirin Gaza.

Tun da farko ƴan tawayen na Huthi sun ce, jirgin da suka kai wa harin, mallakin wani kamfani ne da ke da alaƙa da Isra’ila, abin da ya sa suka yi masa luguden wuta da jirage marasa matuka da kuma manyan makamai masu linzami.

Jirgin dakon man dai, ya taso ne daga Iraqi, inda ya nufi tashar jiragen ruwa ta Athens ɗauke da metric tan dubu 150 na ɗanyen man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)