Mayaƙan Hezbollah sun harba rokoki sama da 200 cikin Isra'ila

Mayaƙan Hezbollah sun harba rokoki sama da 200 cikin Isra'ila

Rahotanni sun ce mutane da dama sun jikkata sakamakon hare-haren na Hezbollah, kamar yadda jami’an Isra’ila suka tabbatar, kodayake basu bayyana adadin wadanda suka ji raunin ba, sai dai jami’an sun yi iƙirarin kakkaɓo akasarin makaman rokar, waɗanda wasu bayanai suka ce akwai waɗanda suka faɗa kusa da birnin Tel Avive.

Ma’aikatar lafiyar Lebanon ta ce ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, mutane fiye da dubu 3 da 750 Isra’ila ta kashe, baya ga jikkata wasu kimanin dubu 15,630 akasarinsu mata da yara, a hare-haren da take ci gaba da kai wa da sunan murƙushe ƙungiyar Hezbollah.

Tashin hankalin da aka shiga, ya sanya ma’aikatar ilimin ƙasar ta Lebanon rufe ilahirin makarantu manyansu da ƙanana har zuwa watan Janairu.

A can birnin Teheran kuwa, Ali Larjani, mai bai wa jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ne ya ce suna nan suna shirin mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ta kai musu a ƙarshen watan Oktoba, makwanni bayan hare-haren da suka kai mata da makamai masu linzami fiye da 200 da zummar jan kunnenta kan yaƙin Gaza.

A gefe guda kuma jagoran addinin a Iran, ya ce kamata yayi kotun duniya ICC ta yanke hukuncin kisa kan shugabannin Isra’ila a maimakon sammacin kamo su da ta bayar a makon jiya, saboda laifukan yaƙi a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)