Mauritius ta kara wa’adin dokar hana fita waje domin yaki da Korona

Mauritius ta kara wa’adin dokar hana fita waje domin yaki da Korona

Kasar Mauritius ta kara wa’adin dokar hana fita wajen da ta saka da zummar magance yaduwar kwayar cutar Korona har izuwa ranar 30 ga watan Afirilu.

Kasar dake kan gabar tekun Indiya mai al’umma miliyan 1.4 a farko ta saka dokar hana fita waje na makonni biyu ne daga ranar 10 zuwa 25 ga watan Maris.

A karkashin dokar hana fita wajen na wuccin gadi an hana yin dukknain taruka haka kuma saka takunkumin rufe fuska ya zama wajibi.

Guraren da aka rufe sun hada da gidajen sinema, guraren wasanni da kuma wuraren dauren aure.

A kasar Mauritius an tabbatar da cewa mutum 12 sun rasa rayukansu sakamakon Korona inda aka samu mutum 1,028 dauke da kwayar cutar Korona kamar yadda jami’ar John Hopskin ta sanar.


News Source:   ()