Matt Gaetz mutumin da Trump ya zaɓa a matsayin ministan shari'a ya janye

Matt Gaetz mutumin da Trump ya zaɓa a matsayin ministan shari'a ya janye

Sanarwar na zuwa ne kwana guda bayan ganawarsa da Sanatoci a ƙoƙarinsu na samun goyon bayansu wajen tabbatar da shi ya jagoranci ma’aikatar shari’a.

Da yawa daga cikin mutanen da Trump ya zaɓa a majalisar ministocin sa -- da kuma shi kansa zaɓeɓɓen shugaban ƙasar na fuskantar zarge zarge masu nasaba da lalata da mata.

Zababben shugaban kasar Donald Trump: Wani alkali a birnin New York ya same shi da laifin cin zarafi da bata masa suna inda daga karshe ya umarce shi da ya biya matar E. Jean Carroll diyyar dala miliyan 83.

Pete Hegseth, wanda aka zaba a matsayin sakataren tsaro: shima wata mata ta shaida wa ‘yan sanda cewa Hegseth ya yi mata fyade a shekarar 2017 bayan da ya dauki wayarta, ya toshe kofar dakin wani otal da ke California kuma ya ki barin ta, a cewar wani cikakken rahoton bincike da aka wallafa. Hegseth ya musanta aikata ba daidai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)