Wani matashin Bafalasdine mai suna Yusuf Nawwaf Muharib ya rasa ransa sakamakon mummunan raunin da ya samu bayan harbin da sojojin Isra'ila suka yi masa a ranar 14 ga Mayu a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaya.
Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin ta fitar ta ce, Muharib da aka harba da harsashan gaske ya mutu a asibitin Ramallah da ake kula da lafiyarsa.
Falasdinawa sun gudunar da bore da zanga-zanga bayan da a watan Afrilu Isra'ila ta kashe mutane da dama tare da jikkata da kama wasu dubunnan a yankunan kasar Falasdinu da daban-daban.