Hukumomi a birnin Ashiya da Tomiko Itooka ke zaune ne suka sanar da mutuwarta tana da shekaru 116.
Itooka tana da yara 4 da jikoki guda 5, tana rayuwa a gidan kula da lafiya na tsofaffi kuma ta mutu a ranar 29 ga watan disambar bara.
Ta koma rayuwa a gidan ne tun shekarar 2019. An haifeta a ranar 23 ga watan Mayu na 1908 a Osaka kusa da Ashiya.
A shekarar 2024 ne aka amince da Itooka a matsayin wadda ta fi kowa daɗewa a duniya bayan mutuwar wadda ta gada ƴar ƙasar Sifaniya Maria Branyas morera mai shekara 117.
Itooka ta yi tsawon rayuwa kuma taga abubuwa da yawa da suka haɗa da yaƙin duniya da annoba da kuma fitowar fasahohi daban-daban a doran duniya.
A lokacin tsufanta tana jin daɗin shan Ayaba da wata shahararriyar madara da ake samarwa a Japan.
Iyaye mata dai na yin tsawon rai a Japan yayin da ƙasar ke fama da ƙaruwar tsofaffi, abin da ke ƙara ta’azzara matsalolin lafiya da kuma ƙaruwar kashe kuɗin kula da walwalar jama’a a ƙasar.
Ya zuwa watan Satumba ƙasar Japan na da mutane dubu 95 da dukkaninsu sun kai shekara 100 ko sama da haka kuma kaso 88 mata ne.
Ƙasar da ke da yawan al’umma miliyan 124 kaso 1 bisa 3 sun kai shekara 65 ko sama da haka a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI