Matar da aka fara yiwa gwajin allurar riga-kafin Covid-19 tana cikin koshin lafiya

Matar da aka fara yiwa gwajin allurar riga-kafin Covid-19 tana cikin koshin lafiya

Matar da aka yiwa allurar riga-kafin kwayar cutar Covid-19 mai suna Jennifer Haller yar shekara 44 a Amurka ta bayyana cewa tana cikin koshin lafiya. 

Haller da aka yiwa allurar riga kafin kwayar cutar Covid-19 a ranar 16 ga watan Maris ta bayyana cewa tana cikin koshin lafiya kuma babu wata matsala tare da ita. 

Jennifer Haller mazauniya garin Seattle dake Amurka ta kasance mace ta farko da aka fara gwajin allurar riga kafin cutar corona a nakasarta. 

A bayanin da Haller ta yiwa manema labarai ta bayyana cewa baya ga dan ciwon kafada bata jin wata matsala. 

Ta kara da cewa tana cikin koshin Lafiya. A yaninda aka tambayeta ko zata sake sadaukar da kanta domin sake gwajin allurar riga kafin cutar corona idan bukatat hakan ta taso, ta kada baki tace ko shakka babu.

 

 

 


News Source:   ()