
Yayin da hukumomin bada agajin na gwamnatin Amurka ke cigaba da miƙa taimakon abinci don magance yunwa ga ƙasashe masu tasowa, kwatsam gwamnatin Amurka ta dakatar da shi, kaɗan bayan shugaba Trump ya sha rantsuwar fara aiki, wanda hakan ya haifar da tsaiko.
Wannan dakatarwar dai, wacce shugaba Trump yayi a ranar 20 ga watan Junairu, ta tsawon kwanaki 90 ce, domin a cewar sa har sai bayan an tantance yadda Amurkan ke bayar da agajin.
Sakataren harƙoƙin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce, har yanzu akwai ɓangarorin agajin da dakatarwar ba ta shafa ba, musamman ɓangaren abinci, sai dai huƙumomin agaji na da shakkun waɗanne bangarori ne dakatarwar bata shafa ba.
Wannan shakkun ya sake ɓullowa ne bayan shugaba Trump ya bada umarnin rufe ofishin huƙumar bunƙasa ƙasashe ta ƙasar USAID.
Har yanzu babu wani bayani a game da shirye-shiryen da za a ci gaba da su, da ma waɗanda aka tsaida saboda jami’an da za su samar da wannan bayani su na hutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI