Mataki na karshe a yakin kasar Libiya

Mataki na karshe a yakin kasar Libiya

Dakarun kasar Libiya na halattaciyar gwamnatin kasar da goyon bayan Turkiyya ta yi nasara akan mayakan janar Haftar a yankunan babban birnin kasar Tripoli, inda ta kuma fara daukar kwararan matakai kai tsaye domin karbe ikon yankuna masu muhinmaci da suka hada da Sirte da Jufra. A daidai hakan ne janar Haftar ya gana da Sisi a Alkahira inda daga bisani ya yi kira da a tsagaita wuta, lamarin da a kallan ke nuna kare matsayin da sojojin kasar suka cimma a yankunan.

 

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Mal. Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA…

 

A yayinda sabili da taimakon da Turkiyya ke baiwa sojojin halatacciyar gwamnatin kasar Libiya ke kara basu kwarin gwiwa da kuma kaisu ga tudun nasara a koada yaushe, mayakan janar Haftar a karon farko suka fara rasa matsayinsu. A lokacin da Turkiyya ta sauke dakarunta a Tripoli da Misrata ne ta fara horar da sojojin Libiya da kuma basu shawarwari da kuma tallafa musu da kayayyakin da suke bukata ne lamurka suka fara sauyawa yadda ya kamata ga gwamnatin kasar. Musamman yadda sojojin kasar suka yi nasara akan mayakan Haftar wajen kwace ikon sararin samaniyyar yankin yammacin kasar daya tilastasu fara ja da baya. A halin yanzu dai garuruwa biyu ne suka rage inda bangarorin biyu ke cigaba da fafatawa da juna. A yankin Sahil dai akwai garin Sirte da kuma wanda ke bangarensa watau garin Jufra.

 

Wadannan garuruwan biyu sun kasance masu muhimmanci ga kasar sabili matatun man fetur din da suke dashi mai dinbin yawa. Dakarun kasar nada niyyar karbe wadannan garuruwan domin mallakar matatun man dake yankunan da kuma  fara haka da fitar da mai zuwa kasashen waje. Sabili da rokon da kasashe kamar su Hadaddiyar Daular Larabawa suka yiwa Janar Haftar an dakatar da hakar mai a wanann yankin.  Da hakan ne aka gurgunta tattalin arzikin gwamnatin kasar ta hanata fitar da kusan ganga miliyan 1.5 lamarin da zai sanya tashin farashin mai a kasuwar duniya. Sabili da haka gabanin gudanar da jarjejeniyar tsagaita wuta ya zama wabiji ga gwamnatin kasar ta fara karbe ikon garuruwan Sirte da Jufra domin mallake ikon matatun man dake yankunan.

 

Baya ga karfafa matakan soja a Libiya matakan siyasa ma na kara tasiri a kasar. Musanman yadda kasashen dake goyawa mayakan Haftar baya kamarsu Hadaddiyar Daular Larabawa, Rasha da Misira suka fara kira da a tsagaita wuta domin kada su cigaba da rasa yunkuna zuwa ga dakarun kasar. Haka kuma abu mafi mahimmanci, ana ganin cewa Janar Hafter ya kasance yana neman wasu 'kawaye bayan rashin nasarar da mayakansa suka fuskanta a hannun dakarun Libiya. Shugaban Majalisar Kasar dake Tobruk Akile Salih na daya daga cikin manyan mutane da ya fara tuntuba. Ita kuwa Turkiyya ta kasance tana daidaita matsayin Rasha da Amurka a Libiya ta hanyar bayar da taimakon siyasa da soja, a inda take kuma kasancewa wata abuyar hadaka ga kasar ta Libiya.  A ‘yan kwankin nan dai ana ganin yadda tsarin Amurka a Libiya ya fara sauyawa zuwa na goyon bayan halattaciyar gwamnatin kasar. Kasancewar yadda jibge sojojin da Rasha ke yi a gabashi ya kasance abin damuwa ga Amurka, ya tilasta ta fara daukar matakai da hadin gwiwar Turkiyya.


Wanan sharhin Mal. Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya…


News Source:   www.trt.net.tr