An gudanar da zanga-zangar kalubalantar shirin mulkin mallakar da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yunkurin yi a tsibirin Sokotra na garin Ebyen da ke kudancin Yaman.
Kungiyoyi masu zaman kansu da suka shirya zanga-zangar da mata suka jagoranta a garin Zencebar da ke karkashin Ebyen sun bayyana cewa,
Suna masu matukar kalubalantar abubuwan da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi a Tsibirin Sokotra da kuma shirin mummunan sulhun da ta yi da kasar Isra'ila.
Masu zanga-zangar dauke da tutocin Falasdinu wadanda kuma suka kone tutar Isra'ila sun rinka rera cea HDL ta fice daga Sokotra.