Masu zanga-zanga sun kone motar 'yan sanda a Arewacin Ireland

Masu zanga-zanga sun kone motar 'yan sanda a Arewacin Ireland

A rikicin da ake ci gaba da yi a Arewacin Ireland wasu gungun masu tarzoma sun kaiwa jami'an 'yan sanda hari inda suka rinka jifarsu da duwatsu.

Tun daga ranar 29 ga watan Maris ne aka fara kalubalantar yarjejeniyar kasuwancin da ke tsakanin Birtaniya da arewacin Ireland bayan ficewar Birtaniyan daga Tarayyar Turai.

Kungiyar dake kalubalantar yunkurin ta hanyar zanga-zanga sun dan yi sanyi bayan mutuwar mijin sarauniyar Ingila Philip amma kuma jin kadan sun sake komawa kan tituna.

Masu tarzomar sun rufe tituna tare da gudanar da kone-kone.

Haka kuma bayan jifar jami'an 'yan sanda da suka rinka yi sun kone mota daya.
 


News Source:   ()