Masu zanga-zanga na ci gaba da matsa wa gwamnati Serbia kan ibtila'in da ya auku

Masu zanga-zanga na ci gaba da matsa wa gwamnati Serbia kan ibtila'in da ya auku

Zanga-zangar da ake mata kallon ta gama gari, na ci gaba da samun karɓuwa a cikin watanni hudun da suka shuɗe, tun bayan mutuwar mutane 15 a lokacin da wani rufi ya faɗa kansu a wata tashar jirgin ƙasa da ke Novi Sad, birni na biyu mafi girma a Serbia.

Yawancin ‘yan ƙasar dai, sun dora alhakin ibtila’in ne kan matsalar cin hanci da rashawa da suke dangantawa da shugaba Aleksandar Vucic, wanda ya shafe tsawon shekaru goma a kan karagar mulki, kuma malamai da manoma da sauran ma’aikata sun shiga sahun masu zanga-zangar da aka ɗauki watanni, inda har ta kai dalibai kauracewa karatu a jami’o’i cikin watan Disamba.

Gwamnatin Vucic, ta ce za ta ƙaddamar da shirin yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da musanta zargin almundahana da ya dabaibaye ɓangaren sufurin jirgin ƙasa.

Ɗaruruwan ɗalibai ne suka yi tattaki zuwa Nis domin gudanar da zanga-zangar, inda suka samu rakiyar mutane sama da 1,500 da ke take musu baya a kan babura.

Firaminista Milos Vucevic da wasu ministoci biyu sun yi murabus, saboda zanga-zangar da ta gudana a babban birnin Belgrade da kuma garuruwan ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)