An sanar da cewa wasu masu neman tada zaune tsaye sun rataye kan alade a kofar Masallacin Vaihingen Enz dake karklashin garin Stuttgart a kasar Jamus.
Tarayyar Hadin Kan Turkawa Musulmi (DİTİB) ta sanar da cewa kamarar tsaro ta dauki bidiyon wasu mutum biyu a yayinda suke rataye kan alade a kofar Masallacin Fatih da misalin karfe 23.30 suka kuma ari na kare bayan yin haka.
Shugaban Masallacin Fati mallakar Hukumar DIBIT dake Vaihingen Enz Latif Pekmezci ya bayyana cewar maharan sun zo ne da wata karamar motar bas mallakar wata kanfani kuma an sanarda 'yan sanda game da lamarin.
Pekmezci, wanda ya bayyana matukar bakin cikin afkuwar lamarin ya kara da cewa 'yan sanda sun fara bincike akan lamarin.