A wata sanarwa da suka fitar yau Lahadi, masu gabatar da kara sun ce, sun gurfanar da Yoon Suk Yeol da tsarewa bisa zargin yunkurin tayar da kayar baya.
A makon jiya ne, masu binciken yaki da cin hanci da rashawa su ka bayar da shawarar gurfanar da Yoon da ke gidan yari, wanda majalisar dokokin kasar ta tsige shi tare da dakatar da shi daga aikinsa.
Lauyoyin Yoon sun bukaci masu gabatar da kara da su gaggauta sakin shi bisa abin da suka kira tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Majalisar dokokin Koriya ta Kudu karkashin jagorancin 'yan adawa ta tsige Yoon a ranar 14 ga watan Disamba, abin da ya sa ya zama shugaba na biyu da aka tsige a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI