Masifu masu alaƙa da sauyin yanayi sun tsananta a 2024 - Ƙwararru

Masifu masu alaƙa da sauyin yanayi sun tsananta a 2024 - Ƙwararru

Alƙaluman da masana suka fitar dai sun bayyana shekarar 2024 a matsayin wadda yanayin zafi yafi tsananta sama da waɗanda suka gabace ta, abinda ya sa a cikin watan Yuni mutane fiye da 1,300 suka rasa rayukansu saboda tsananin zafin da ya kai maki 51.8 bisa ma’aunin Celcius a Saudiya, yayin aikin Hajjin da ya gabata.

A Pakistan kuwa tsananin zafin ya tilasta killace miliyoyin yara a gida, sai kuma tashin gobarar daji da ya raba dubban mutane da muhallansu a Girka, da yammacin Amurka da kuma Canada, inda alƙaluman masu bibiya suka ƙiyasta cewar aƙalla sau dubu 400 aka samu tashin gobarar daji a sassan ƙasashen Kudancin Amurka tsakanin watan Janairu zuwa Satumban shekarar 2024 mai ƙarewa.

Dangane da ambaliyar ruwan kuwa, ba za a manta da iftila’in da ya afka wa ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ba a cikin watan Afrilu, lokacin ambaliyar ta mayar da sassan ƙasar da dama tamkar harshen teku.

Haka dai iftila’in na ambaliya ya riƙa afkawa sassan duniya inda a tsakanin Yammaci da tsakiyar Afrika kaɗai rayukan mutane sama da dubu 1,500 suka salwanta, yayin da wasu fiye da miliyan 4 suka rasa muhallansu.

Ana gaf da ƙarƙare wannan shekara ta 2024 ne kuma tsibirin Mayotte da Mozambique suka fukanci mummunan iftila’in guguwar Chido, inda aƙalla mutane 200 suka mutu, ko da yake a iya cewa Philippines ta fi jin jiki domin a watan Nuwamba kaɗai sau shida ta gamu da masifun guguwar.

A Kudancin nahiyar Afirka kuwa aƙalla mutane miliyan 26 ne suka tagayyara sakamakon iftila’in fari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)