Masar za ta sake bude kofar Refah da ke iyakarta da Zirin Gaza

Masar za ta sake bude kofar Refah da ke iyakarta da Zirin Gaza

Masar ta amince da bude kofar shiga da fita ta Refah da ke tsakaninta da yankin Zirin Gaza na Falasdin.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Gaza Iyad Al-Buzum ya shaida cewa, a ranar Lahadin nan za a bude kofar Refah inda za a dinga shiga da fita Gaza ta kofar.

Tun watan Mayu zuwa yau, ranar 22 ga Agusta ne karo na farko da ka rufe kofar Refah don shiga da fita Zirin Gaza ba tare da wani dalili ba.


News Source:   ()