Durkushewar igiyar ruwan AMOC, wato wani igiyar ruwan da ke ɗaukar ruwa mai ɗumi daga arewacin tekun Atlantic, kana ya samar wa da nahiyar Turai yanayi mara cutarwa, zai iya b jefa halin rayuywar al’ummar yankin Arctic da sauran su a cikin hatsari, a cewar masana kimiyyar.
A wata wasiƙa da su ka aike wa majalisar ministoci ƙasashen yankin na Nordic da su ka haɗa da Denmark, Sweden da wasu yankuna 3 masu cin gashin kansu, masana kimiyya sun ce, irin wannan sauyin da ke shafar igiyar ruwa yana da mummunan tasiri da ba za a iya warwarewa ba, musamman ga ƙasashen nordic da ma wasu sassan duniya.
Masannan sun buƙaci majalisar ministocin ƙaksahsne su ɗauki mataki da zai haɗa da yin kira zuwa ga rage yawan hayaƙi mai gurbata muhalli da ake fitarwa a ƙasashen nasu.
Bincike da aka gudanar da dama sun nuna cewa ana matuƙar raina irin hatsarin da ke tattare da sauyin igiyar ruwan AMOC ta tekun Atlantic, a ceewar masanan, inda su ka ƙara da ceewa akwai yiwuwar wannan hatsari zai zarta maƙura a cikin ƴan gwamman shekaru masu zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI