Yayin tsokacinsa, shugaban Amurka Joe Biden bayyana Yahya Sinwar ya yi a matsayin katangar da ya hana cimma muradun samar da zaman lafiya a Gaza. Yayin da Firaministan Canada Justin Trudeau ya ce mutuwar Sinwar sakayya ce ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin ranar 7 ga Oktoban bara.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Ministan Harkokin Wajen Jamus kuwa cewa suka yi, dama ta samu na sakin dukkanin mutane da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su, sai kuma kawo ƙarshen mummunan halin al’ummar Gaza ke ciki.
Sai dai a iya cewa ya yi wuri a iya hasashe ko hangen samun kwanciyar hankali nan kusa a Gaza, saboda alwashin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya ce, nasarar da suka samu ba ta nufin za su sassauta hare-haren da suke kaiwa, matsayin da masu bibiyar lamurra ke ganin babban tarnaki ne ga shirin Amurka na maido da zaman lafiya a Gaza.
Tuni Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoran nata, yayin da ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta sha alwashin zafafa farmakin da take kaiwa Isra’ila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI