Martanin ƙasashe kan ƙudirin MDD da ya haramtawa Isra'ila mamayar Falasɗinu

Martanin ƙasashe kan ƙudirin MDD da ya haramtawa Isra'ila mamayar Falasɗinu

A yammacin jiya Laraba ne zaman babban zauren ya amince da wannan ƙudiri wanda ƙasashe 124 suka goyi bayansa wasu 14 suka ƙalubalance shi a ɓangare guda 43 suka ƙauracewa zaman, lamarin da ya baiwa majalisar damar amincewa da shi kai tsaye.

Wannan mataki na Majalisar ya nunawa Isra’ila ba sani ba sabo lura da yadda za ta fuskanci takunkumai matuƙar bata janye daga yankunan da ta mamaya cikin shekara 1 da ta gabata ba a wani yanayi da ya rage kwanaki a faro taron babban zauren na Majalisar wanda shugabannin ƙasashe ke da kwanaki 6 cur don gabatar da jawabansa kan duk wani ƙalubale da ya shafe ƙasashensu ko kuma wani sashe na duniya.

Tuni dai jakadan Falasɗinu a zauren Majalisar Riyad Mansour ya yi maraba da ƙudirin wanda ya bayyana shi da mafarin nasarar ƙoƙarinsu na samun ƴanci yayinda jakadan Isra’ila Danny Danon ke cewa abin kunya ne yanke makamancin hukuncin.

Shi kuwa shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas cewa ya yi akwai buƙatar ƙasashen duniya su matsa ƙaimi ga Isra’ila don ganin ta mutunta hukuncin, yayinda Hamas a nata ɓangaren ta yi maraba da matakin.

A ɓangare guda Amurka ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ya fifita Falasɗinawa akan Isra’ila yayinda Qatar ta bayyana matakin majalisar a matsayin adalci ga al’ummar Falasɗinu.

Itama ƙungiyar ƙawancen ƙasashen yankin Gulf da suka ƙunshi Bahrain da Kuwait da Oman da Qatar da Saudi Arabia baya ga hadaddiyar daular larabawa maraba ta yi da wannan mataki na Majalisar wanda ta ce shi ne zai tabbatar da ƴancin Falasɗinawa.

 A ɓangare guda ƙungiyar ƙasashen musulmi ta OIC mai mambobi 57 ta ce Falasɗinawa na da cikakken ƴanci kamar kowanne yanki mai cin gashin kansa, yayinda ƙungiyar tarayyar Turai ke cewa ya zamewa zauren wajibi ya tabbatar da ƴancin Falasɗinawa kamar kowanne ɗan adam.

Su ma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam irin Amnesty International da Human Right Watch sun goyi bayan wannan ƙudiri tare da neman bin diddigi don ganin Isra’ila ta mutunta shi tare da hukunta ta matuƙar aka same ta da karya doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)