Ƙasashe da dama sun mayar da martani game da kisan na Nasrallah inda masana ke ganin zai sake zafafa yaƙin da yanzu haka Isra’ilan ke gwabzawa da ƙungiyoyi masu samun goyon bayan Iran irinsu Hezbollah da Hamas da kuma Houthi.
Shugaba Joe Biden ya yi maraba da kisan Nasrallah wanda ya bayyana da adalci, haka zalika mataimakiyar shugaban Amurka kuma ƴar takarar neman kujerar shugabancin ƙasar wadda ta ce an kawar da guda cikin manyan barazana a gabas ta tsakiya.
Shi kuwa mataimakin shugaban Iran Mohammad Reza Aref gargaɗi ya yi da cewa kisan Sayyed Nasrallah zai zama farkon rushewar Isra’ila kuma ƙarshen ta’addancinta ga yankin na gabas ta tsakiya.
Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da makokin kwanaki 5 don jimamin mutuwar jagoran na Hezbollah.
A ɓangare guda Rasha waddata alaƙanta kisan da rikicin siyasa ta buƙaci Isra’ila ta gaggauta janyewa daga hare-haren da ta ke kaiwa Lebanon tare da yin ala wadai da kisan wanda ta ce zai sake ta’azzara rikicin gabas ta tsakiya.
Ministan harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta shaidawa gidan talabijin na ARD fargabar yiwuwar kisan ya sake tarwatsa tsaron ilahirin ƙasar ta Lebanon wanda kuma baya daga cikin muradan Isra’ila.
Shi kuwa Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres bayyana matuƙar damuwarsa ya yi da abin da ya kira yanayin sauyawar halin da ake ciki a Beirut cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Ƙungiyar Hamas wadda Hezbollah ta tsunduma yaƙin baya-bayan nan da Isra’ila saboda ita, ala wadai ta yi da hare-haren Isra’ila a Lebanon da kuma yadda ta ke kisan fararen hula, abin da ta ce shi ne babban aikin da yahudawan suka sanya a gaba.
Ita kuma gwamnatin yankin Falasɗinu ta bakin shugaba Mahmud Abbas miƙa saƙon ta’aziyyarta ta yi ga Lebanon kan kisan na Nasrullah.
A ɓangare guda ƴan tawayen Hutsi na Yemen bayyana Nasrallah ta yi da shahidi ta na mai cewa kisan na shi ba zai karya musu gwiwa ba face zaburar da su wajen ci gaba da farmakar Isra’ila.
A nasa ɓangaren shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya wanda har yanzu ya na da kyakkyawar hulɗar diflomasiyya da Isra’ila cewa ya yi sam bai kamata kisan ƙare dangin da Isra’ila ke aikatawa ya shafi Lebanon ba, ba tare da ya kama sunan Sayyed Nasrallah ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI