Kungiyar da ke aiki a China wacce Amurka ta sanya wa jerin takunkumi ta mayar da martani ga gwamnatin Washington.
Bayanai daga shafukan sadar da zumunta na Qihoo 360, daya daga cikin manyan kamfanonin riga-kafin software da samar da cibiyoyin sadarwa a China, ya ce Amurka ta siyasantar da lamarin.
An bayyana cewar,
"Qihoo 360 ya nuna adawa sosai ga wannan dabi'ar mara ma'ana da al'adar Kasuwanci ta Amurka ke aiwatar da siyasa da bincike kan ci gaban kimiyya da fasaha."
A ranar 22 ga watan Mayu, Ma'aikatar Kasuwanci ta Amurka ta sanar da cewa kungiyoyi 24 na kasar China suna cikin jerin takunkumi bisa dalilan cewa suna da hannu cikin ayyukan da ba su dace da tsaron kasa ko bukatun manufofin kasashen waje ba.
Ma'aikatar ta kuma ba da sunayen wasu kungiyoyi 9 na kasar China a jerin takunkumi na take hakkin bil adama da Turkawan Uyghur da ke yankin Sincan Uyghur mai cin gashin kanta.