Jam’iyyar CHP ta yi kakkausar suka ga mujallar Faransa (Charlie Hebdo) wacce ta buga zanen da ke kwaikwayon Shugaba Recep Tayyip Erdogan da ke nuna dabi’u marasa kyau.
Mataimakin shugaban jam’iyyar CHP, Engin Altay a Babban Taron Majalisar Dokokin Turkiyya (TBMM) da ya ke magana da manema labarai ya bayyana ra’ayinsa game da zanen da Charlie Hebdo ta buga.
Altay ya jaddada cewa sukar da aka yi wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bata musu rai kuma ba za su taba yarda da su ba.
Babu wani mutum ko wata kasa wacce zata zagi kasarmu da mu ke kauna ko shugaban kasarmu ko Hadisin mu. Ba mu yarda ba. Ba za mu amince da hakan ba. Za mu mayar da martani mai tsauri kamar yadda aka yi a baya a majalisar dokoki tare da biyayya ga doka. Bugu da kari, babu wani, ba wata kasa, ba shugaban kasa ko kafafen yada labarai da za su iya yin girman kai na cin mutuncin Musulunci da Annabinsa, sauran addinai da Annabawa. Sauya fasali a cikin addinin Musulunci ba batun Macron bane. A gaskiya cewa buƙatar sauya fasali a cikin Musulunci ta fito ne daga wani kamar Macron girman kai ne da tsaurin ido. Kowa zai san iyakarsa. Koda kuwa zane ne, ba zai yiwu mu yarda da sukar da aka yi wa 'yancin mutane a matsayin ’yancin tunani ba. Zanen da ke kwaikawayon Annabinmu da shugaban kasar Turkiyya rashin hankali ne kuma abu ne mai matukar muni.