Mark Zuckerberg ya faɗi yadda ya sha matsin lamba daga gwamnatin Amurka lokacin annobar Covid-19

Mark Zuckerberg ya faɗi yadda ya sha matsin lamba daga gwamnatin Amurka lokacin annobar Covid-19

A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 26 ga watan Agusta Mark Zuckerberg  ya faɗawa kwamaitin majalisar wakilan Amurka cewa yayi da na sanin rashin yin magana kan matsin lambar da ya sha daga gwamnatin Amurka  da ma wasu matakai da ya ɗauka a matsayinsa na mamallakin kafafen sada zumunta na Facebook da Instagaram da Whatsapp na cire wasu bayanai a shafukan.   

A 21 ga watan Ulin 2021 shugaban Amurka Joe Biden ya ce kafafen sada  zumunta kamar Facebook na kashe mutane saboda barin bayanan ƙarya da ake yaɗawa kan cutar Corona da ma allurar rigakafi.

Wasu mutane kamar tsohon sakataran yaɗa labaran fadar white House Jen Psaki da babban mai bayar da shawara kan sha’anin lafiyar Amurka Vivek Murthy sun fito fili tare da cewa matakan da kamfanin na Facebook ke ɗauka sun yi kaɗan kuma batun na kara wahala wurin magance cutar.

Shafin Facebook a wancan lokaci ya ce suna ɗaukar matakai masu tsauri kan irin waɗannan bayanai. Gwamnatin shugaban Amurka Biden ta rage caccakar batun duk kuwa da ci gaba da sharara ƙarya iri-iri kan allurar rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)