Manufofin hare-haren da PKK ta kaiwa Peshmerga

Manufofin hare-haren da PKK ta kaiwa Peshmerga

A lokacin da Turkiyya ta zafafa yaki da ta’addanci a arewacin Iraki, da alama kungiyar ta’addar PKK ta kara kaiminta kai tsaye akan Peshmerga da sojojin  Gwamnatin Yankin Kurdawan Iraki (KRG). A harin da ta kai a baya bayanan ma sojojin Peshmerga 7 suka rasa rayukansu inda wasu da dama kuma suka jikkata. Haka kuma su ma gwamnatin yankin Kurdawan Iraki sun dauki kwararan matakan yaki da kungiyoyin ta'addanci da suka hada da PKK .

 

Akan wannan maudu'in mun sake kaucewa tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA.

 

A yan kwanakin nan da rundunar sojin gwamnatin yankin Kurdawan Iraki da Peshmerga suka kara kaimin yaki da ta'addanci, kungiyar ta'addar PKK a yankin Amedi dake gundumar Duhok ta kara yawan hare-haren da take kaiwa sansanin Peshmerga. A harin da ta kai kwanakin bayan nan ma ta kashe dakarun Peshmerga 6 da kuma raunana wasu da dama. A wani harin da suka kai a wata sansanin kuma jami'in Peshmerga 1 ya rasa rayuwarsa. Bayan wannan harin dakarun gwamnatin yankin Kurdawan Iraki sun kara kaimin farmakai da suke kaiwa kan yan ta'addar PKK, inda kuma ita PKK ta fara yada farfagandar dake nuna cewa ba ta da alhakin kai hare-haren.

A bayanin da PKK ta fitar ta yi ikirarin cewa ta ja kunnen dakarun Peshmerga da kar su shiga yankin Metina, a bayanan kuma ta musunta hare-haren da ake zarginta da kaiwa. Amma kuma dukkan alamomi na nuna cewa PKK na daukar matakan kalubalantar Peshmerga. Shugabanin gwamnatin yankin Kurdawan Iraki har ma da firaiminista Barzani sun zargi PKK inda suka sukabalanceta da kakkausar murya.

 

ldan muka dubi baya zamu iya ganin alamun cewa wadanan tashin tashinan sun afku ne sannu a hankali. Da farko dai gudunmowar da Peshmerga ta baiwa dakarun kasar Turkiyya a yakin da ta kaddamar akan PKK a yankunan Avashin-Basyan da Metina ya haifar da fadawar PKK cikin mawuyacin hali. Baya ga kauda da yawan mambobin kungiyar ta'addar, an kuma karbe ikon wasu yankunan dake hannunsu tare da hanasu amfani da yankunan da suke kai-kawo. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya sanya suka haifar da kai hare-hare akan Peshmerga domin sun ci gaba da nuna kwanjinsu.

 

A karshe dai, kungiyar ta'addar ta kaddamar da farmakai na kin kari da suka ba ta damar mallake yankuna da dama tare da kuma daukar matakan da gwamnatin yankin Kurdawan Iraki ba za ta amince dashi ba. Kimanin kauyuka 700 na karkashin ikon PKK. Wannan yanayi ne da gwamnatin yankin Kurdawan Iraki musanman bangaren KDP ba za ta amince dashi ba. Hakika matakan da rundunar sojin Turkiyya ta dauka akan kungiyar ta'addar PKK zai zama wata babbar dama ga KDP.

Alamomi dai na nuna cewa Peshmerga za ta cigaba da yaki da kungiyar ta'addar PKK tare da kuma taimakawa Turkiyya a yaki da dukkan ta'addanci.

 

 

Wannan sharhin Mal Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya. Ku huta lafiya..


News Source:   ()