Mamakon ruwan sama a Japan

Mamakon ruwan sama a Japan

An yi gargadin za a kwashe jama'a daga yankunansu tare da dakatar da safarar jiragen kasa a Japan saboda mamakon ruwan sama.

Hukumar Kula da Yanayi ta Japan (JMA) ta fitar da gargadi ga jihohin Hokkaido, Aomori, Iwate da Gifu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ci gaba da yi.

JMA ta sanar da guguwa za ta yi gudun kilomita 90 a Hokkaido, kilomita 80 a Tohou da Hokuriku.

Tashar Talabijin ta Kasa ta Japan (NHK) ta bayyana cewa, an bayar da gargadin kwashe mutane dubu 2,405 a Iwate, dubu 8,399 a Aomori da wasu dubu 1,204 a Hokkaido.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Japan ta bayyana an dakatar da safarar jiragen kasa a wasu a Tokaido.

 


News Source:   ()