Malaysia ta dakatar da zirga zirgan jiragen sama tsakaninta da kasar lndiya sanadiyar sabuwar nau'in kwayar cutar Korona da ta bulla a ķasar.
Ministan harkokin tsaron kasar Malaysia lsmail Sabri Yakub ne ya sanar da matakan da kasar ta dauka akan sabuwar nauin korona mai lamba B.1.617 da ta bulla a ķasar lndiya.
Ministan ya bayyana cewa kasar Malaysia ta yanke hukuncin dakatar da dukkanin jirga jirgan jiragen sama tsakaninta da kasar lndiya.
Ya kara da cewa za'a hana shigowar har da lndiyawan dake aiki a ķasar Malaysia. Bugu da kari za'a kuma dakatar da shigowa da kayayyaki daga lndiya na dan wani lokaci.