Makomar shugaban Korea ta kudu ta shiga tararrabi bayan tsanantar bore

Makomar shugaban Korea ta kudu ta shiga tararrabi bayan tsanantar bore

Makomar shugaba Yoon Suk Yeol ta shiga tararrabi ne tun bayan yunkurinsa na sanya dokar Soji da ta harzuƙa jama’a, a wani yanayi da a farko ɓangaren adawa ne kaɗai ke kiraye-kirayen buƙatar murabus ɗinsa, gabanin juyewar lamarin zuwa na ƙasa baki ɗaya, inda ko a jiya cikin gaggawa ministan tsaronshi Kim Yong-hyun ya sanar da murabus wanda tuni shugaban ya maye gurbinsa da wani.

Yoon wanda ya karɓi ragamar jagorancin Korea ta kudu a shekarar 2022, idan har ya tabbata matsin lamba ya tilasta masa murabus, zai zama shi ne shugaban farar hula na farko da jama’a suka tilastawa shugaba sauka daga mulki a baya-bayan nan, bayan shirin dawo da wannan doka da ba a yi amfani da ita a ƙasar ba cikin fiye da shekaru 40 da suka gabata.

Rahotanni sun ce bayan ƙaƙƙarfan gangamin da masu zanga-zangar bisa jagorancin ɓangarorin adawa suka gudanar a dandalin Gwanghwamun da ke tsakiyar birnin Seoul wani tsagi na masu zanga-zangar ya ɓalle zuwa ofishin shugaban da nufin matsa lamba.

Tun farko babbar jam’iyyar adawar Korea ta kudun da mambobinta suka tayar da rikici a zauren majalisa tare da shiga faɗa da sojojin da suka shigo zauren ne don aiwatar da dokar ta Soji, ita ta fara neman lallai shugaba Yoon ya yi murabus bayan da ta ce bai cancanci jagorancin ƙasar ba.

Kowanne lokaci a gobe Juma’a ne ake saran jin ko shugaba Yoon zai yi murabus ko akasin haka, a wani yanayi da ɓangaren adawar mai rinjayen mambobi 300 a zauren majalisa ke neman tsirarin mambobin jam’iyya mai mulki da za su ɓalle don haɗewa da ita da nufin samun kashi 2 bisa 3 na majalisar don aiwatar da ƙudirin tsige shugaban cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)