Majalisar Peru ta amince akan binciken ko sinadarin bleach na maganin Korona

Majalisar Peru ta amince akan binciken ko sinadarin bleach na maganin Korona

'Yan majalisar kasar Peru sun amince da a fara binciken ko sinadarin ruwan (bleach) zai iya maganin annobar Korona ta hanyar shansa ko kuma yin allurarsa.

Yayinda aka amince da kudirin tare da kuri’u 49 da 39, hukuncin da majalisar ta yanke ya sha suka daga kungiyar kwararru ta musamman da kuma wasu jam’iyyun siyasa.

Ed Malaga-Trillo, dan majalisa na jam'iyyar Purple Party kuma masanin kimiyyar jijiyoyi, ya kira hukuncin da abin kunya.

Masana kimiyya daga ko'ina cikin duniya sun yi gargadin cewa ruwan (Bleach) wanda ake amfani dashi a masana'antu kamar tsabtace kayan aikin likita, tsabtace injunan masana'antu, wankin tufafi, ko goge itace da kayan masaku; amfani dashi a cikin jikin bil adama ta ko wace fanni zai haifar lalcewar koda, haifar da matsalar numfashi, zubar jini a cikin binl adama da zasu iya haifar da mutuwa nan take.


News Source:   ()