Wannan dai na daga cikin yarjejeniyar farko da aka fara cimmawa, gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da za a fara gadan-gadan daga gobe Talata, inda shugabannin ƙasashe za su sanya mata hannu.
A karkashin yarjejeniyar da taron ya amince da ita, shugabannin sun yi alƙawarin ƙarfafa tsarin da ke tsakanin su don ci gaba da kawo sauye-sauye a duniya, da kuma kare muradun al'ummar yanzu da na wacce za ta zo nan gaba, waɗanda ke fuskantar kalubale.
Yarjejeniyar ta kuma bukaci kawo sauyi game da cibiyoyin hada-hadar ƙudi na duniya, da Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da samar da haɗin gwiwa wajen magance matsalar sauyin yanayi da kuma inganta tsarin ƙirƙirarriyar fasaha.
To sai gun-gun ƙasashen Belarus da Korea ta Arewa da Iran da Nicaragua da kuma Syria ƙarƙashin jagorancin Rasha, sun bukaci kara sauya fasalin yarjejeniyar, sai dai hakarsu bata cimma ruwa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI