Karo na farkon kenan da irin haka ta faru a Faransa cikin shekaru 62, bayan rusa gwamnatin Fira Minista Georges Pompidou da majalisa ta yi a 1962.
Ƙudirin kaɗa ƙuri’ar yankan ƙauna ga gwamnatin da Banier ke jagoranta, ya samo asali ne bayan da sabon Fira Ministan da aka naɗa a watan Satumba, ya tsara kasafin kuɗin kula da walwalar jama’a ba tare da sa hannun ƴan Majalisa ba, ya kuma nemi yi musu ƙarfa-ƙarfa kan su amince da kasafin, abinda ya sanya jam’iyyar New Popular Front ta masu sassaucin ra’ayi da kuma ta National Rally ta masu kishin ƙasa shan alwashin kawo ƙarshen gwamnatinsa.
Jim kaɗan bayan ƙuri’ar da suka kaɗa ne kuma, masu sassaucin ra’ayi suka buƙaci shugaba Macron yayi murabus, domin bayar da damar shirya zaɓen sabon shugaban ƙasa.
Sai dai yayin tsokaci kan rikita-rikitar da siyasar Faransa ta shiga, gabanin fitar sakamakon yankan ƙaunar a daren yau, shugaba Emmanuel Macron da ke kan hanyar komawa gida daga Saudiya, yayi watsi da rahotannin da ke cewa zai yi murabus.
Macron ya ce babu abinda zai hana shi ƙaraasa wa’adin shugabancinsa zuwa shekarar 2027, duk da ƙaruwar kiraye-kirayen neman ya sauka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI