Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta rawaito cewa za ta tattauna kan halin da Gimbiya Latifa, wacce ta ce mahaifinta Sarkin Dubai ya yi garkuwa da ita, ke ciki da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Kakakin Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya kan Kare Hakkin Dan Adam, Rupert Colville ya bayyana cewar tabbas za su tattauna batun tare da Hadaddiyar Daular Larabawa bayan fitowar bidiyon Gimbiya Latifa a jiya.
Kakakin ya jaddada cewa sauran cibiyoyin da ke karkashin tsarin Majalisar Dinkin Duniya na kare hakkin dan adam na iya shiga tsakani bayan bincika bidiyon.
A halin yanzu, a cikin bayanin da Kungiyar Majalisar Dinkin Duniyar da ke aiki kan kama mutane ba bisa ka'ida ba ta fitar, an lura da cewa za a iya fara gudanar da bincike bayan an kammala bincika bidiyon.
‘Yar mataimakin shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Firaminista kuma Sarkin Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid al Maktoum, Gimbiya Latifa ta zargi mahaifin nata da yin garkuwa da ita bayan ya kama ta lokacin da take kokarin guduwa daga kasar a shekarar 2018 a cikin bidiyon da ta aika wa kawayenta.
A cikin bidiyon da aka dauka a asirce a cikin 'yan watannin bayan faruwar lamarin, Latifa ta ce an yi garkuwa da ita kadai a wani gidan da aka rufe tagogi da kofofi da ‘yan sanda ke ba wa kariya, ba tare da samun magani ko taimakon shari'a ba.
An kama Gimbiya Latifa a gabar tekun Indiya kuma an dawo da ita yayin da take kokarin barin kasar ta hanyar teku a shekarar 2018 tare da taimakon wani Bafaranshe.
Da yawa daga cikin masu kare hakkin dan adam a duk fadin duniya sun bayyana cewar an dauke Latifa da karfi zuwa kasar kuma hakan "satar ta ne."