Mahukuntan Amurka sun fara gyaran ɓarnar da guguwar Milton ta yi a Florida

Mahukuntan Amurka sun fara gyaran ɓarnar da guguwar Milton ta yi a Florida

A hukumance tuni aka fara aikin yashe dattin da guguwar ta tattara akan tituna baya ga dawo da lantarkin da ta kashe wanda ya jefa kusan mutum miliyan 16 a tsananin duhu.

Alƙaluma sun nuna cewa mutane 16 guguwar ta Milton ta kashe a sassan birnin Florida.

Wasu magidanta da ke gyaran matsuguninsu bayan lafawar guguwar Milton a jihar Florida. Wasu magidanta da ke gyaran matsuguninsu bayan lafawar guguwar Milton a jihar Florida. © JOE RAEDLE / Getty Images via AFP

Duk da cewa guguwar ba ta yi ɓarnar da ka yi hasashen za ta tafka a jihar ta Florida, amma bayanai na nuna cewa ana buƙatar aƙalla dalar Amurka biliyan 100 gabanin kammala gyaran ɓarnar da ta yi.

Zai dai ɗauki makwanni zuwa watanni gabanin kammala gyaran muhallan jama'a waɗanda yanzu haka ke rayuwa a matsugunan wucin na gidajen tafi da gidanta da gwamnatin jihar ta Florida ta samar musu.

Makamantan guguwar dai ba sabon abu ba ne a jihar ta Florida inda ko a makwanni 2 da suka gabata aka ga makamanciyar guguwar da aka yiwa laƙabi da Helene wadda ita ma ta haddasa gagarumar ɓarna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)