An yi gargadi ga yankuna 51 a Faransa saboda afkuwar wata mahaukaciyar guguwa dake rushe gidaje.
Hukumar Kula da Yanayin Sama ta ba da rahoton cewa za a ga walkiya, ruwan sama da ƙanƙara saboda guguwar, kuma saurin iska na iya kaiwa kilomita 100 cikin sa'a ɗaya.
A garin Saint-Nicolas de Bourgueil da ke Indre-et-Loire, hasumiyar kararrawar coci ta ruguje saboda iska mai karfi kuma rufinsa ya zube.
Daga cikin yankuna da gargadin ta shafa har da babban birnin Paris da lardunan da ke kewaye da ita.