Mahara sun kashe mutum biyar a Afghanistan

Mahara sun kashe mutum biyar a Afghanistan

An kashe mutane biyar a wani hari da makami da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afghanistan.

Ferdevs Faramarz, kakakin ofishin ‘yan sandan Kabul, ya ce wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan mutane 5 a yankin Guldere a Kabul.

Da yake bayyana cewa mutane 5 wadanda 2 daga cikinsu jami'an tsaro ne sun mutu sakamakon harin, Faramarz ya bayyana cewa maharan sun tsere daga yankin.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.


News Source:   ()